Gidan uncle hausa novel complete 1
Barka da shigowa wannan gida mai tarin albarka, wannan ƙasaitaccen littafi na gidan uncle ko nace gidan ankul complete, littafi ne wanda yayi shura a wasu shekaru da suka gabata, wanda makaranta da dama sun nuna sonsu ga wannan littafi kama daga gidan uncle page 11-20, wasu kuma a kafar yanar gizo sunfi bukatar gidan uncle 80 and 72, ko shakka babu Boss Bature tayi kokari wanda ba zai misaltu ba sakamakon irin basirar data nuna wajen kaddamar da wannan ƙasaitaccen littafi na gidan ancul, duk da cewa a wannan gida bamu bayar da cikakken littafin ba, amma akwai wajajen da zaku iya samun novel din gidan uncle complete ku sauke izuwa cikin wayoyinku na salula domin shakatawa da ɗebe kewa. A ƙasa shine abinda zamu iya kawowa.
Bayan Hameed ya gama magana, sai yayi baya da karfi, yana jin wani zafi mai tsanani a zuciyarsa. Ya cigaba da fadin, “Yaya za ayi ku ce na saki matata? Me tayi min da zan rabu da ita, alhalin itace rayuwata? Daddy, wallahi Umaimah tana yankar jikina, tana cin ni, ban san yadda zan rayu babu ita ba. Wallahi bansan sanda na rubuta takardar sakin nan ba. Ban san me ya faru da ni ba. Jiya na kwanta a dakin Bloody, amma da safe sai na tashi na ganni a dakin Salma. Wallahi Daddy, ban san komai akan wannan takarda ba. Don Allah, ku dubi halin da nake ciki, ku ji tausayina, kada ku rabani da matata."
Yayin da yake magana, muryarsa ta rinka kakkaryewa saboda tashin hankali. Daddy ya taso da sauri ya zaunar da shi akan kujera, sannan ya dora masa Ahmad Shuraif akan cinyarsa. Daddy ya ce, “Hameed, abin da ya faru ya riga ya faru. Ka saki Umaimah a daren jiya, kuma a wannan daren ta tsarkaka daga iddarka. Wannan yaron kuma rabonsa ne ya haifar maka. Na shiga tsakani da sunan mahaifinku marigayi, don haka yanzu ka yi hakuri.”
Daddy ya shige daki, sai kuma Hajiya ta rufe dakin da Umaimah take ciki da mukulli. Ta tafi kitchen tana shirin girki, amma ta fito bayan awa daya ta tarar da Hameed yana zaune, ya rungume yaron a jikinsa, numfashinsa yana sarqawa. Bata ce komai ba, ta wuce daki.
Gidan uncle complete part 2
Lokacin da Hajiya ta bar wajen, sai Hameed ya tashi da kyar ya shiga dakin da Umaimah take. Ya tsaya a bakin kofa yana kallonta, idanunsa sun kada sun yi jawur. Tana kwance rufe da bargo, tana shasshekar kuka. A hankali ya karasa ya zauna kusa da ita, sai ya ji tana fadin, "Innalillahi wa inna ilaihir raji’un." Ya janye bargon, sai tayi saurin dagowa suka hada ido, amma ta kawar da nata cikin sauri.
Yana kokarin rike hannunta, sai ta make shi da karfi tana cewa, “Kada ka tabani, Hameed! Na haramta gareka har abada. Wallahi Allah zai saka min akan wannan bakin cikin da ka jefani ciki. Na yi danasanin saninka, kuma bantaba jin tsanarka ba irin yanzu. Allah ya isa tsakanina da kai.”
Hajiya ta fito daga daki a lokacin, tana ganin abinda ke faruwa sai ta nuna Hameed da hannu tana cewa, “Ka tashi ka fita daga nan!” Hameed ya dago yace, “Hajiya, ku saurare ni! Meyasa koda yaushe ni ake dora wa laifi? Me nayi da kuka ki kula da halin da nake ciki?”
Hajiya ta yi murmushi mai ciwo tana cewa, “Ka tafi wurin matarka Salma. Wannan gidan ba naka bane yanzu." Ta turashi waje ta rufe qofar.
Rashin Kwanciyar Hankali
Hameed ya durkushe a bakin kofa yana kiran sunan Umaimah, hawayen zafi suna zuba daga idanuwansa. Daga baya ya mike da kyar, ya shiga mota yana kuka. Sai da ya isa gidan abokinsa Yusuf sannan ya samu ya fara magana.
“Yusuf, wallahi Daddy ya ce ni da kaina na saki Umaimah saki biyu! Ban san yaushe hakan ya faru ba. Ban taba yin abu haka ba.” Yusuf ya tsorata, yana tambayar, “Hameed, ya za a ce ka saki matarka alhalin baka cikin hayyacinka?”
Hameed ya cigaba da kokawa da zuciyarsa, har ya fara zubar da jini daga bakinsa. Yusuf ya yi kokarin taimaka masa, amma Hameed ya nace, yana cewa, “Ka kaini gida. Bana son asibiti. Rayuwa babu Umaimah bata da ma’ana."
Fada da Salma
Bayan sun koma gida, Hameed ya rubuta takardar sakin Salma. Ya nufi dakin ta tare da wata belt, ya fara jibgarta. Duk da tana kuka tana neman taimako, bai daina ba sai da ta sume. Daga nan ya cilla mata takardar sannan ya fita daga gidan.
Yayin da yake kokarin shiga motar Yusuf, sai ya fadi. Yusuf da megadi suka taimaka masa suka dauke shi zuwa asibiti. Likitoci sun cigaba da kula da shi, amma halin da yake ciki ya sa zuciyarsa na barazanar faduwa.
Kar a sha'afa cewa mun sanar da cewa ba lallai bane a samu cikakken littafin gidan uncle complete domin saukewa anan gidan ba muna godiya.