Tarihin Sokoto Birnin Shehu

Tarihin Sokoto Birnin Shehu

Wannan munyi shine akan tarihin Sokoto Birnin Shehu, dama wasu abubuwa masu alaƙa kamar tarihin kofofin Sokoto da tarihin wasu gwamnonin jihar Sokoto.

Tarihin Sokoto Birnin Shehu

Tarihin masarautar Sokoto

Gabatarwa
:

Daular Sokoto wacce a wani lokacin akan kira da suna daular Usmaniyya, ta samo asali ne bayan jahadin Shehu_Usmanu_bin_Fodiyo tun a farkon ƙarni na goma sha tara (19).

A can wani zamani a baya, tun a farkon ƙarni na goma sha shida (16), a kewayen wasu koguna da ake cewa kogin Rima da kogin Sokoto anyi wata shahararriyar daula wacce ake kira Kanta ko kuma Kebbi, wadda sarki Kanta Kota ya mulka. Wannan daula har saida tayi bunƙasar da tana iya nunawa daular Borno yatsa saboda gawurtarta wanda kuma a wannan lokaci daular Borno tana ƙarƙashin mulkin ‘Mai Ali’. Ƙarfin iko da izza na wannan daula ya ɗaukaka har zuwa ƙasar Agadas. Haka dai ƙarfin wannan daula ya cigaba da wanzuwa na tsawon ɗaruruwan shekaru, kamar yadda bayanan Last (1977) suka ruwaito.

To kasan ance a rayuwa kome kake dashi dole wata rana zai zama babu domin kuwa a  farkon ƙarni na goma sha takwas (18), tauraruwa da ƙarfin iko na wannan daula ta Kebbi ta dusashe, sannan wata daular kuma mai suna Zamfara Allah ya ɗaukakata. Wannan kuwa ya samo asali ne sakamakon harin da ita daular Zamfarar ta kai izuwa daular Kebbi kuma ta samu nasara a kanta. Waɗannan dauloli guda biyu sun wanzu a cikin wannan duniya kowacce tana jin ta isa, duk da cewa ƙarfin daular Zamfara ya danne na daular Kebbi, amma dai kowace daula daga cikinsu ta isa da kanta. Daular Kebbi tana yamma da kogin Neja, daulolin Zamfara da daular Gobir suna daga gabashin kogin na Neja.

Wannan babban kogi na Neja a cikinsa mutanen waɗannan dauloli guda uku suke gudanar da sana’ar (Su) wacce muka fi sani da kamun kifi. Duk da cewa akwai wasu koguna biyu wato kogin Rima da kogin Sokoto, amma su wadatar kifin dake cikinsu bai isa yin sana’a ba  ga jama’a na waɗannan dauloli.

Bayanin Last (1977) ya ruwaito cewa, a sannu a hankali waccan daula ta Zamfara ta dinga faɗaɗa tana ƙara girma, har saida takai tafi kowace daula ƙarfin faɗa aji a wannan nahiya gaba ɗaya, wacce a zuwa ƙarshen ƙarni na goma sha takwas (18), saida ta mamayi harshi kanshi yankin kogin Rima.

Irin wannan ƙarfin iko na daular Zamfara, bai tsawaita sosai ba, daga baya itama daular Gobir ta danne ta. Wannan daula ta Gobir sai data faɗaɗa tayi girman da tazararta da nisanta da birnin Zamfara bai haura mil ashirin da biyar ba (25) daga Arewa maso Gabas.

A farkon ƙarni na goma sha tara (19), itama wannan daula ta Gobir ta durƙushe. Sakamakon durƙushewar wannan daula ta Gobir, shine ya kawo kafuwar sabuwar daular Musulunci mai hedikwata a Sokoto (masomin tarihin Sokoto birnin Shehu ) wadda wannan sabuwar daula ta musulunci saida ta haɗiye dukkan waɗancan dauloli guda uku masu ƙarfi wato (Zamfara, Kebbi da Gobir) har dama wasunsu, kamar yadda wannan rubutu namu ya dauki aniyar yin bayani daki-daki akan tarihin Sokoto birnin Shehu.

Ƙasar Hausa: a tarihin Sokoto birnin Shehu Wikipedia (pdf).

Kasantuwar wannan babbar daula ta musulunci mai hedikwatarta a Sokoto ta tsiro ne a ƙasar Hausa, yana da matuƙar muhimmanci a ɗanyi magana a dangane da wannan yanki na ƙasar Hausa.

Ƙasar Hausa dai wani yanki ne dake cikin Afirka. Ya kasance wani yanki da Larabawa suke kira ‘Biladi_Sudan’, wato ma'anar wannan suna shine garurun baƙaƙe. Yanki ne mai faɗin gaske a cikin Afirka. A wannan yanki na garuruwan baƙaƙe ƙasar Hausa keda yanki mafi girma. Wanda faɗinta yana farawa ne tun daga tafkin Chadi ta gabas kenan, ta runtuma har izuwa tsakiyar ƙasar Nijar daga yamma kenan (wato idan kaje ka tsaya a bakin tafkin Chadi, sai ka juyo da gabanka yamma har saika kai tsakiyar ƙasar Nijar duk a cikin ƙasar Hausa kake, wanda kuma ya kasance duk yanki ne na garuruwan baƙaƙe) wannan shine dalilin da yasa zaka ji fiye da kaso tamanin cikin ɗari na mutanen Nijar hausawa ne. Haka zalika tana da faɗin sama da mil dubu ɗaya da ɗari biyar daga yammaci, sannan kuma kuma sama da mil dubu biyu daga gabashi (Johnston, 1967). (mun faɗaɗa bayani ne a cikin tarihin Sokoto birnin Shehu).

Wannan yanki na garuruwan baƙaƙe, yasha samun kutse daga Larabawa yadda ya kamata waɗanda keda manufa ta mulkin mulkiya, sannan kuma sunata tatsar arziƙin ƙasa a fannin kasuwanci da wasu harkokin tun wajen ƙarni na shida kafin daga baya kuma a farkon ƙarni na ashirin Turawan mulkin mallaka su shigo. Wannan shine babban dalilin da yasa zaka ga cewa wayewar ƙasar Hausa ya sako asaline daga Larabawa, musamman ta fuskar al’adunmu da addini.

Zuwan Jarumi Bayajidda ƙasar Hausa, na ɗaya daga cikin abubuwan da ake kallo a matsayin tushen wayewa ta wannan ƙasa ta Hausa. A wannan lokaci an samu kafuwar wasu manyan masarautu guda bakwai da aka yiwa laƙabi da Hausa bakwai a ƙasar Hausa sakamakon zuwan Bayajidda. Waɗannan masarautu sune kamar haka: Daura, Kano, Rano, Zazzau, Katsina, Garun-Gabas, da kuma masarautar Gobir.

Bayan kafuwar waɗannan masarautu masu girma, an kuma samun kafuwar wasu manyan masarautun daban waɗanda suka yi ƙarfi suma sosai. Su kuma waɗannan masarautu su aka yiwa laƙabi da Banza Bakwai. Daga cikin waɗannan masarautu akwai Zamfara, Kebbi, da kuma Yawuri.

Tarihin kofofin sokoto

Tun asali dai birnin Sokoto ya kunshi ƙofofi guda takwas ko kuma tara a wata faɗar amma a mafi ingancin magana ƙofofin Sokoto guda takwas ne.

Domin waziri Junaidu Allah yayi masa rahama: yace ƙofofin birnin Sokoto guda takwas ne kuma sun zama takwas ne domin kyakkyawan fata ga ƙofofin aljannah.

Waɗannan ƙofofi na tarihin Sokoto sune kamar haka: 

Guda biyu suna gabashin birnin Sokoto wanda sune:

1. Ƙofar Rini 

2. Ƙofar Marke 

Biyu kuma suna yammacin Sokoto:

3. Kofar Kade 

4. Ƙofar Aliyu Jode 

Biyu Kuma suna Kudancin birnin Sokoto wato:

5. Kofar Taramniya

5. Ƙofar Atiku

Sauran biyu kuma suna bangaren arewa wato:

7. Ƙofar Kware 

8. Ƙofar Dundaye 

Waziri Junaidu Allah ya ƙara rahama a gareshi yace: Asalin kofofin birnin Sokoto an yisu da itatuwa ne sai kuma daga baya a zamanin sarkin musulmi Aliyu Babbah aka mayar dasu ƙofofin ƙarfe. 

Ƙofofi guda biyu an jingina sunayensu ga mutanen kirki guda biyu wato ƙofar Atiku da kofar Aliyu Jode. Kuma anyi hakanne domin kasancewar gidajensu na kusa da waɗannan ƙofofin. 

Ƙofofi guda biyu kuwa an jingina sune zuwa ga garuruwa waɗannan sune ƙofar Kware da ƙofar Dundaye dalili kuwa idan zaka je waɗannan ƙofofi a kanbi ta hanyar wannan garuruwa ne.

Sauran ƙofofi huɗu kuwa an jigina sune ga sunayen wasu itatuwa ko muce bishiyoyi.

Tarihin gwamnonin jihar Sokoto

Tarihin Usman Faruk - gwamnan jihar Sokoto

Ya kasance Kwamishinan ’yan sanda (wanda yayi ritaya) Usman Faruk (an haife-shi a shekara ta alif ɗari tara da talatin da uku 1932 A.C) a lokacin Miladiyya. shine Gwamna a matsayin Soja na farko a Jihar Arewa maso Yamma a Najeriya daga shekarar 1967 zuwa shekara ta 1975 bayan ta ɓalle daga tsohuwar jahar arewa a lokacin mulkin soja na Janar Yakubu Gowon. Janar Murtala Muhammad wanda ya karɓi mulki a juyin mulki a ranar ashirin da tara -29 ga julin shekara ta 1975 ne ya koreshi daga muƙaminsa, sannan kuma ya ƙaddamar da binciken daya sameshi da laifin wadatar da kansa ba bisa ƙa'ida wato a lokacin da yake kan mulki. Daga baya kuma gwamnatin Ibrahim Badamasi Babangida ta mayar dashi bakin aiki bayan an wanke shi akan tuhume-tuhumen da ake yi masa, kuma an bashi cikakken albashinsa da muƙamin ritaya. Ya bar mulki jihar ta rabu zuwa Jihar Neja da Jihar Sokoto.

Tarihin general Umaru Mohammed -gwamnan jihar Sokoto

An nada Laftanar Kanar (daga baya Birgediya) Umaru Mohammed Gwamnan Jihar Arewa maso Yamma a Najeriya a watan Yulin shekara ta 1975 a farkon mulkin soja na Janar Murtala Mohammed . A watan Fabrairun shekara ta 1976 an raba Jihar Arewa maso Yamma zuwa Jihar Neja da Jihar Sakkwato . Umaru Mohammed ya cigaba da aiki a matsayin gwamnan Jihar Sakkwato har izuwa Yulin shekara ta dubu ɗaya da ɗari tara da saba'in da takwas 1978.

Tarihin Shehu kan Giwa -gwamnan jihar Sokoto

Alhaji Muhammadu Shehu Kangiwa shine zababben farar hula wanda yayi gwamna na farko a jihar Sokoton Nijeriya a cikin gajeren zango na biyu a ƙasar ta Nijeriya, Kuma ya riƙe wannan mukamin daga watan Oktoban shekara ta alif dari tara da saba'in da tara 1979 zuwa watan Nuwamban shekara ta alif dari tara da tamanin da ɗaya 1981. Ya wakilci jam'iyyarsa ta National Party of Nigeria (N-P-N). Ya kasance gwamna abun yabo daga sassa daban-daban na ƙasa, mai bayar da ruwa, kiwon lafiya ga jama'arsa, shigar da harkar noma cikin kasafin jiha, samar da ilimi a dukkan matakai da kuma yin gaskiya a  gwamnatinsa.

Tarihin Garba Nadama -gwamnan jihar Sokoto

Garba Nadama (ya rayu daga 1938 - zuwa 4 ga Mayun shekarar 2020) mashahurin ɗan siyasar Najeriya ne wanda yayi aiki a matsayin gwamnan farar hula na biyu a jihar ta Sokoto, shima kuma bai jima ba wato cikin ɗan gajeren lokaci a Jamhuriyyar Najeriya ta Biyu, ya riƙe wannan muƙamin ne daga Janairun 1982 zuwa Nuwamban shekarar alif dubu daya da dari tara da tamanin da uku 1983. Wato shine ya gaji Shehu Kangiwa, wanda ya rigamu gidan gaskiya a hatsarin Polo.

Tarihin Garba Duba -gwamnan jihar Sokoto

Garba Duba (anyi haihuwarsa a shekara ta 1942) tsohon sojane wanda yayi wa Najeriya aiki a matsayin Laftanar Janar mai ritaya kuma yayi gwamnan jihar Bauchi da farko, daga Yulin shekarar dubu ɗaya da ɗari tara da saba'in da takwas 1978 zuwa Oktoba 1979 duk a lokacin mulkin soja na Janar Olusegun_ Obasanjo, kuma shidin ya kasance mai gudanarwa na jihar ta Sokoto daga Janairun shekarata 1984 zuwa Agustan tamanin da biyar 1985 a lokacin soja. a lokacin gwamnatin Manjo Janar Muhammadu Buhari.

Tarihin Garba Mohammed -gwamnan jihar Sokoto

shidin kanar ne kafin (daga baya Birgediya Janar kuma) Garba Mohammed (ya rayu daga 15 Afrilu 1944 – zuwa 10 ga Afrilu 2021 ) an naɗa shi a matsayin gwamnan jihar Sokoto daga watan Agustan shekara ta alif dari tara da tamanin da biyar 1985 zuwa Disambar shekara ta 1987 a zamanin mulkin soja na Janar Ibrahim Babangida wato IBB.

Tarihin Ahmed Muhammad Daku -gwamnan jihar Sokoto

Ahmed Muhammad Daku (an samu haihuwarsa a shekara ta alif ɗari tara da arba'in da hudu 1944) shima kuma birgediya janar ne na sojan Najeriya sannan mai ritaya wanda yayi gwamnan mulkin soja na jihar Kano daga watan Agusta na shekarar dubu ɗaya da tamanin da biyar 1985 zuwa Disambar shekarar __1987. Daga baya kuma ya hau a matsayin Gwamnan Soja na Jihar Sakkwato daga Disambar shekarar __1987 zuwa Agusta na shekarar __1990.

Tarihin Bashir Salihi Magashi -gwamnan jihar Sokoto

Tsohon janar ne na sojan Najeriya, Kuma shi yayi ministan tsaro a zamanin mulkin Buhari, wanda shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ɗora shi. Yayi gwamnan jihar ta Sokoton Najeriya a shekara ta alif dari tara da casa'in daidai 1990 zuwa 1992 a lokacin mulkin IBB wato Ibrahim Babangida.

Tarihin Yahaya Abdulkarim gwamnan jihar Sokoto

Yahaya Abdulkarim (an haife_shi a_ranar 21_ga watan Agusta, shekara ta alif_ɗari tara da arba'in da_hudu_1944), cikakken ɗan siyasar Najeriya ne wanda yayi aiki a matsayin jihar Sokoto, tsakanin watan Janairun shekara ta 1992, zuwa watan Nuwamban shekara ta 1993, a lokacin ƙoƙarin Janar Ibrahim Badamasi Babangida zuwa mulkin dimukuraɗiyya. Bayan komawar Najeriya dimokuraɗiyya a shekara ta alif dari tara da casa'in da tara 1999, ya zama mai mulki a jam'iyyar People Democratic Party reshen jihar Zamfara, kuma yayi aiki na wani ɗan lokaci a majalissar ministocin shugaba ƙasa Obasanjo.

Tarihin Yakubu Mu'azu -gwamnan jihar Sokoto

Birgediya _Janar_Yakubu_Mu'azu_wanda 
faka fi sani da_Kanal_ne_ya kuma_kasance Mai_Gudanarwa_na_Jihar ta_Sakkwato, daga ranar 9 ga watan_Disamba_shekarar 1993 zuwa ranar 22 ga watan Agusta na shekara ta alif dari tara da casa'in da shida 1996. A lokacin _mulkin soji.

Tarihin Rasheed Adisa Raji -gwamnan jihar Sokoto

Rasheed Adisa Raji yayi shugaban mulkin soja na jihar Bauchi daga ranar 14 ga Satumba alif dari tara da casa'in da huɗu 1994 zuwa 22 ga watan Agustan casa'in da shida 1996 sannan kuma ya koma jihar Sokoto daga 22 ga watan Agusta casa'in da shida 1996 zuwa Agusta casa'in da takwas  1998 a lokacin mulkin soja na Janar Sani_Abacha.

Tarihin Attahiru Bafarawa -gwamnan jihar Sokoto

Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa an samu haihuwarshi a ranar huɗu 4 ga watan Nuwamba na shekara ta alif _(1954A.C) a yanayin Miladiyya. Ya kasance gwarzon dan siyasan Najeriya ne wanda yayi gwamnan ɗaya daga cikin jihohin Hausa wato jihar Sakkwato daga ranar 29 ga watan Mayu na shekarar dubu daya da ɗari tara da casa'in da tara 1999 zuwa ranar 29 ga watan Mayu na shekarar dubu biyu da bakwai 2007.

Aliyu Magatakarda Wamakko -gwamnan jihar Sokoto

Aliyu Magatakarda Wamakko an samu haihuwarshi a ranar ɗaya 1 ga watan Mayu, na shekarar (1953) kuma ɗan siyasane da aka zaɓe shi a matsayin gwamnan jihar daular Sakkwato da take shiyyar arewa maso yammaci a cikin ƙasar Nijeriya a watan Afrilun shekara ta dubu biyu da bakwai 2007, a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PDP (people democratic party) wacce ake fi sani Lema.

Tarihin Aminu Waziri Tambuwal -gwamnan jihar Sokoto

Aminu Waziri Tambuwal anyi haihuwarsa a ranar goma 10 ga watan Janairu, a shekarar alif ɗari tara da sittin da shida _(1966) a yanayi na miladiyya, a garin Tambuwal dake ɗaya daga cikin yankunan kudancin jihar Sakkwaton Najeriya, kuma shi ɗin ya fito ne daga zuri’ar Wazirin masarautar ta Tambuwal.

Manhajar teburi ɗauke da jerin sunayen gwamnonin Sokoto.👇

SunaMatsayiShiga ofisBarin ofisJam'iyyaKarin bayani
Alhaji Usman FarukGwamna a soja19671975SojaKwamishinan yan sanda na Northwestern State
Colonel Umaru MohammedGwamna a sojaMayu 1976Juli 1978Soja
Lt. Colonel Gado NaskoGwamna a sojaJuli 1978Oktoba 1979Soja
Shehu KangiwaGwamna a farar hulaOktoba 1979Nuwamba 1981NPN
Garba NadamaGwamna a farar hula1982Disamba 1983NPN
Colonel Garba DubaGwamna a sojaJanuri 1984Agusta 1985Soja
Colonel Garba MohammedGwamna a sojaAgusta 1985Disamba 1987Soja
Colonel Ahmed Muhammad DakuGwamna a sojaDisamba 1987Agusta 1990Soja
Colonel Bashir Salihi MagashiGwamna a sojaAgusta 1990Januri 1992Soja
Malam Yahaya AbdulkarimGwamna a farar hulaJanuri 1992Nuwamba 1993NRC
Colonel Yakubu Mu'azuMai Gudanarwa9 Disamba 199322 Agusta 1996Soja
Navy Captain Rasheed Adisa RajiMai Gudanarwa22 Agusta 1996Agusta 1998Soja
Group Captain (Air Force) Rufai GarbaMai GudanarwaAgusta 1998Mayu 1999Soja
Attahiru BafarawaGwamna a farar hula29 Mayu 199929 Mayu 2007APPANPP
Aliyu Magatakarda WamakkoGwamna a farar hula29 Mayu 200711 Afrilu 2008PDP
Abdullahi Balarabe Salamegwamna na riƙon ƙwarya11 Afrilu 200828 Mayu 2008-
Aliyu Magatakarda WamakkoGwamna a farar hula28 Mayu 200828 Mayu 2011PDPLawal Muhammad Zayyana gwamna mai aiki
Aliyu Magatakarda WamakkoGwamna a farar hula28 Mayu 201128 Mayu 2015APC
Aminu Waziri TambuwalGwamna a farar hula28 Mayu 201529 Mayu 2023APC/PDP
Ahmad AliyuGwamna a farar hula29 Mayu 2023Kan aiki

Post a Comment

0 Comments